Namadi Sambo ya ƙaryata komawarsa jam’iyar APC

0
126
Namadi Sambo ya ƙaryata komawarsa jam'iyar APC

Namadi Sambo ya ƙaryata komawarsa jam’iyar APC

Daga Idris Umar, Zariya

A wani sakon gaggawa mai ɗauke da sa hannun
Umar Sani
Tsohon mai ba da shawara kan harkokin yada labarai ga Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Arc. Mohammed Namadi Sambo, ya sanyawa hannu ya ƙaryata komawar tsohon shugaban kasar jambiyar APC kai tsaye.
Takardar tace Hankalina ya kai ga wata jita-jita da ke yawo a kafafen yada labarai da ke cewa Mai Girma, Arc. Mohammed Namadi Sambo, GCON, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa na Tarayyar Najeriya, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Wannan magana karya ce, babu gaskiya ko kadan a cikinta.

KU KUMA KARANTA: APC ta musanta cewa Ganduje ya sha da ƙyar a Gombe

Sakamakon yawan kira da tambayoyi da aka rika yi, da izinin iyalan Mai Girma, na ga dacewar fitowa da wannan sanarwa don karyata wannan jita-jita. Ina jaddada cewa wannan labari ƙarya ne da aka ƙulla da mugunta domin yaudarar jama’a.

Hoton da ake yadawa a matsayin hujja — wanda ke nuna Mai Girma tare da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani — ba sabon hoto bane. An ɗauke shi shekaru da suka gabata lokacin da Gwamnan ya kai masa ziyarar ta’aziyya a gidansa da ke Abuja, bayan rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sani Sambo. Yanzu ana ƙoƙarin amfani da hoton cikin makirci domin ƙirƙirar ƙarya.

Haka kuma, Mai Girma zai halarci bikin kaddamar da asibitin kwararru mai gado 300 da ke Kaduna a ranar Alhamis, 19 ga Yuni, 2025. Wannan aiki ne da ya fara lokacin da yake kan mulki, kuma yana nuni da cikakken sadaukarwarsa ga cigaban Jihar Kaduna da walwalar al’umma. Gayyatarsa zuwa wajen taron da yiwuwar yin jawabi ba su kamata a fassara su a matsayin goyon bayan siyasa ko alamar sauya sheka ba.

Don kaucewa duk wani rudani, muna tabbatar da cewa Mai Girma, Arc. Mohammed Namadi Sambo, har yanzu mamba ne mai biyayya da ƙwazo a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP). Bai sauya sheka ba, kuma babu wani shiri ko niyya da yake da shi na shiga wata jam’iyya. Labarin sauya shekar dai ƙirƙira ne kawai da nufin tayar da kura da neman ɗan kananan tagomashi na siyasa.

Muna roƙon jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da wannan ƙarya, su kuma yi mata kallon raini da kaskanci kamar yadda ta dace.

Leave a Reply