Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki – UNICEF

0
99
Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki - UNICEF

Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki – UNICEF

Daga Shafaatu Dauda Kano

Asusun tallafawa ƙananun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (Unicef) ya bayyana cewa Najeriya ce ke da mafi yawan yara masu fama da matsanancin ƙarancin abincin masu gina jiki a nahiyar Afirka.

A cewar sanarwar da asusun ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Talata, daga cikin yara 10 da ke fama da wannan matsala biyu ne kawai ke samun magani.

Asusun ya bayyana cewa kimanin yara miliyan biyu ne a Najeriya ke fama da matsalar ta tamowa, inda hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan yaran da ba su girma yadda ya kamata kuma ta biyu a duniya, da kashi 32 cikin 100 na yara ‘yan ƙasa da shekara biyar.

KU KUMA KARANTA:Masu ƙwacen waya a Kano sun kashe ɗalibin Jami’ar Bayero

Hakazalika, Unicef ya ce kashi 7 cikin 100 na mata masu haihuwa a Najeriya na fama da matsanancin ƙarancin abinci.

Asusun ya nuna damuwa kan yadda ƙarancin abinci ke haddasa kashi 45 cikin 100 na mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekara biyar tare da barazana ga lafiyar jama’a da tattalin arziki.

Leave a Reply