Nafisa Abdullahi: Yawan kuɗinta da kadarorinta

0
613

Tana ɗaya daga cikin jaruman fina-finan Kannywood masu hazaƙa da farin jini. Adadin dukiyar da Nafisa Abdullahi dai batu ne da ake tattaunawa akai, idan aka yi la’akari da irin nasarorin da ta samu a masana’antar da sauran harkokinta.

Ana hasashen Jarumar dai tanada mallakin Naira miliyan 500. An haife ta ne a ranar 23 ga watan Junairu 1991. Nafisa ta samu digiri a fannin wasan kwaikwayo a jami’ar Jos kuma cikin sauri ta fara wasan kwaikwayo a shekarar 2010, tare da Ali Nuhu a cikin fitaccen fim ɗin Sai wata rana.

Ta samu rigingimu sosai, har yakai ga dakatar da ita daga Kannywood saboda shigar banza. Wasu daga cikin fina-finanta sun haɗa da; Kalamu Wahid, Siriin da ke raina, Munafikin mata, Dan marayan zaki, Madubin sakamakon, Mai farin jini, da kuma shirin fim ɗin Hausa mafi shahara mai suna Labari na.

Nafisa Abdullahi ta samu lambobin yabo da dama da suka haɗa da kyautar gwarzuwar jarumar fim a shekarar 2013, da lambar yabo kamfanin nishaɗantarwa ta City People da kuma lambar yabon kamfanin MTN gwarzuwar jaruma ta Kannywood a shekarar 2014. Wannan a zahiri ya kai ga samun ɗaukakar darajar Nafisa Abdullahi.

A shekarar 2021, Nafisat Abdullahi ta ƙaddamar da kayan kwalliyarta mai suna ‘Naf cosmetics’ Abuja, wanda yaci miliyoyin Naira. Sanan kuma tana da shagon tufafi; Naf closets, da wurin shaƙatawa na cafe dake Jos mai suna Larous_cafe. Baya ga haka, ita ce ta kafa kamfanin Nafs Entertainment, kamfanin shirya fina-finai.

Nafisa Abdullahi jakadiya ce a kamfanin Tpumpy estates Abuja, wani kamfani ne na gidaje, da kuma Salis Drive, da kuma kamfanin lemon kwalba na Pepsi. Ba abin mamaki ba ne yadda Nafisa ta kasance cikin jin daɗin rayuwa don an haife ta a cikin dangi masu arziki kuma, tsawon shekaru, ta sami kuɗin kanta.

Idan aka yi la’akari da motocinta, gidajenta, sana’o’in hannu, kasuwancin ta, da yawan tafiye-tafiye, Nafisa Abdullahi tana da kimanin naira miliyan 500. Tana da manyan gidaje da motoci masu tsada sosai. Yanzu haka tana tuƙa mota ƙirar Chevrolet Cruze 2019 mai farashin Naira miliyan 20 tare da wata mota ƙirar Mercedes Benz ta kimanin Naira miliyan 16.

Leave a Reply