Na yi nadamar sauya halitta ta: Wata mata ta koka kan yadda laɓɓanta ke ta kara girma

0
533

Wata mata wacce ta so mayar da leɓenta kamar yadda take a baya, bayan biyan likita maƙudan kuɗaɗe don ya sauya mata shi, tana fama bayan leɓenta ya koma tamkar balam-balan, LIB ta ruwaito.

Karli Gardner ta ce sai da tayi gwaje-gwajen asibiti wanda ya nuna mata babu wata matsala don ta yi gyaran a leɓenta, hakan ya bata damar amincewa da likita yayi mata aikin.

Sai dai tana fama don tun da aka yi aikin laɓɓanta su ka ci gaba da girma tamkar ana hura su.

Yayin da take bayyana halin da take ciki a TikTok, Karli ta ce ta ci gaba da gyaran duk da dai bata ji daɗin yadda laɓɓanta su ka yi manya ba bayan kammala aikin.

A cewarta: “ina nan ina fama da kai na, na yi gwaje-gwaje a asibiti kuma an ga cewa babu wata matsala, amma ga halin da nake ciki yanzu.”

Ta ci gaba da cewa: “Wannan ma aya ce ga masu son kara girman laɓɓansu.”

Cike da hawaye, Karli tace ba ta son yadda su ka koma duk da bayan an ƙara mata girmansu ta yi ƙoƙarin mayar da su yadda suke a baya amma sai ci gaba suke yi da girma.

Leave a Reply