Na daina jin daɗin rayuwa, jiran lokacin mutuwa nake- Aminu Ɗantata

0
274

Shahararren attajirin nan na jihar Kano kuma hamshakin ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata, ya bayyana cewa yanzu baya jin daɗin rayuwa, kuma yana fatan ya bar duniya cikin aminci da salama

Aminu Ɗantata mai shekaru 91 ya kuma nemi gafarar waɗanda yayi wa laifi kamar yadda ya ce shi na yafe wa waɗanda suka yi masa laifi idan akwai.

Ya bayyana haka ne a ranar talata, a lokacin da ya karɓi baƙuncin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, a gidansa da ke unguwar Ƙoki a ƙwaryar birnin Kano.

Ya ce shekarun baya ya zagaya faɗin Najeriya inda ya gana da mutane da kuma samun abokai a kusan dukkan jihohin tarayyar ƙasar nan amma da kyar ya iya kiran mutum 10 da ke raye cikin abokan nasa a yau.

“Na zagaya duk jihohin Najeriya kuma na yi abubuwa da mutane a duk faɗin jihohin, da yawa abokai na ne amma abin baƙin ciki, duk mutanen da na sani, da kyar na iya ƙiran guda 10 da ke raye.

KU KUMA KARANTA:Tinubu/Shettima: Wannan tikitin babbar nasara ce ga Jam’iyyar APC – Gwamna Buni

“Gaskiya, kamar yadda nake a yanzu, ina jiran lokaci na ne kawai, bana jin daɗin rayuwa a yanzu, Ina fatan na bar duniya da imani.

“Ina fata ban ɓata wa kowa rai ba a rayuwa, Idan na ɓata wa wani rai, ina fatan su gafarta mini. Idan wani ya yi mini laifi, na yafe ma shi.

“Yanzu ni kaɗai ne na rage a cikin iyalina da ke zaune da jikoki,” in ji shi.

Aminu Ɗantata, wanda kawu ne ga Aliko Ɗangote, hamshakin attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afrika, ya yabawa Shettima kan ziyarar.

Shettima, wanda ya kai ziyarar a jihohin Jigawa da Kano, ya ce ziyarar na da nufin ganawa da dattawan jihohin biyu kan ayyukan ci gaba da ake yi a yankin arewa gabanin zaɓen 2023.

Ya kasance a jihar Jigawa ranar litinin, inda ya gana da sarakunan Hadeja, Adamu Abubakar-Maje; Sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi; Sarkin Gumel, Ahmed Muhammad-Sani; Sarkin Kazaure, Najib Husseini-Adamu da Sarkin Ringim, Sayyadi Abubakar-Maumud.

Leave a Reply