Mutuwar Sarkin Gobir: Mun miƙa komai ga Allah – Iyalansa

0
42
Mutuwar Sarkin Gobir: Mun miƙa komai ga Allah - Iyalansa

Mutuwar Sarkin Gobir: Mun miƙa komai ga Allah – Iyalansa

‘Yan Najeriya na ci gaba da yin tir da yadda har aka yi ‘yan ta’addar daji suka kashe Mai Martaba Sarkin Gobir.

Iyalan na Sarkin Gobir Isa Muhammad Bawa da ma al’ummar daular Gobir na ci gaba da nuna alhini akan rashin Sarkin, wanda ‘yan bindiga suka kashe bayan ya shafe sama da sati uku hannunsu.

Yanzu haka ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna alhininsu akan rashin marigayin wanda Allah ya yi wa cikawa, duk da ƙiran da ya yi na a ceci rayuwarsa kafin ya bar duniya.

Da misalin ƙarfe goma da rabi na daren jiya Laraba ne dukkan dangin marigayi Sarkin Gobir suka tabbatar da cewa Sarkin ya bar gidan duniya.

Tun da misalin ƙarfe biyu na rana ne aka fara samun labarin rasuwar sa ta hannun Magajin Garin Gobir Shua’ibu Gwanda Gobir.

Sai dai duk a lokacin dangin sa ba su sallama suka tabbatar da kisan sa ba, kamar yadda Ɗansa Sirajo Isa Bawa Turakin Gobir ya ke bayani.

Bayan tabbatar da rasuwar ta sa iyalansa sun samu kansu cikin ruɗu da tashin hankali a cewar wasu daga cikin su.

Hajiya Ummah, mai ɗakinsa, ta bayyana cewa, sun kaɗu ainun da samun wannan tabbacin mutuwar Sarki.

Ita kuma Aisha, wadda ke zaman diya ga sarkin, ta ce shi ne gatansu, yanzu kuma ya bar duniya Allah ya bi masa hakkinsa ga masu hannu ga mutuwar ta sa.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir, Isa Bawa 

Al’umma dai a Sabon Birni na ci gaba da zaman zullumi tare da jaddada kira duk da yake sun jima suna yin kiran ba a yi komai ba har ta kai cin rayuwar sarki.

‘Yan Najeriya dai yanzu haka suna ci gaba da nuna alhini akan wannan lamarin, kamar yadda suke ta wallafawa a shafukan yada zumunta na yanar sadarwa.

Tsohon mataimakin Shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, na daga cikin muhimman mutane da suka yi Allah wadai da jan kafa da gwamati ta yi har wannan lamarin ya faru, kamar yadda shafin gidan radiyo na bbc ya wallafa.

Daidai lokacin hada wannan rahoto babu hukumar da ta fito fili ta yi magana ko ta’aziya akan rashin basaraken.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here