Mutum 33 sun mutu bayan da motarsu ta faɗa cikin kogi a Kenya

0
468

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Aƙalla mutum 33 ne suka mutu, wasu da yawa suka jikkata lokacin da wata mota maƙare da fasinjoji ta fada cikin kogin Nithi a kasar Kenya.

Hukumomin ƙasar sun samu nasarar kuɓutar da mutum 10, a hatsarin da ya auku ranar Lahadi da daddare.

Motar dai na kan hanyarta ta zuwa birnin Mombasa daga garin Meru.

‘Yan sanda sun ce binciken farko da aka gudanar ya gano cewa burkin motar ne ya shanye lokacin da take tsaka da gudu.

Ana ci gaba da aikin ceto, yayin da ake tunanin adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa.

A ‘yan shekarun nan dai ana samun yawaitar hatsarin mota a titunan ƙasar Kenya.

Leave a Reply