Mutane da dama a Congo sun mutu a wani yunƙurin fasa gidan yari

0
33
Mutane da dama a Congo sun mutu a yunƙurin fasa gidan yari

Mutane da dama a Congo sun mutu a wani yunƙurin fasa gidan yari

Gwamnatin Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan harin da aka kai gidan yarin Makala, da ke babban birnin Kinshasa, kasar cikin daren jiya.

Shedun gani da ido sun ce harin fasa gidan yarin da aka kai ya yi sanadiyar mutuwar gwamman mutane, duk da dai gwamnatin ƙasar ta ce mutane biyu kawai suka rasa ransu.

Kakakin gwamnatin ƙasar, Patrick Muyaya wanda ke cikin tawagar shugaban kasar Felix Tshisekedi da ke China don halartar taro, ya ce manyan jami’an tsaron kasar sun isa wajen da abin ya faru don tabbatar da dai-daiton lamura.

Ministan shari’ar kasar Constant Mutamba, ya ce suna nan suna gudanar da bincike don hukunta wadanda ke da wannan wajen kitsa fasa gidan yarin.

KU KUMA KARANTA: Fursunoni sun tsere daga gidan yarin Nijar da ke tsare da masu ta da ƙayar baya

Wannan dai ba shine karo na farko da ake kaiwa gidan yarin harin ba, domin ko a shekarar 2017 sai da aka fasa shi inda kusan fursunoni dubu 4 suka tsere.

Shi dai gidan yarin na Makala an gina shine da zummar daukar fursunoni dubu daya da dari 5, sai dai alkaluman hukumomin kasar na nuna cewa akwai kimanin fursunoni dubu 14 zuwa 15 da ake tsare da su a ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here