Mutane 400,000 a arewacin Ethiopia na fuskantar barazanar zabtarewar ƙasa 

0
36
Mutane 400,000 a arewacin Ethiopia na fuskantar barazanar zabtarewar ƙasa 

Mutane 400,000 a arewacin Ethiopia na fuskantar barazanar zabtarewar ƙasa

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ake ci gaba da sheƙawa a yankin Amhara da ke arewacin ƙasar Habasha ya jefa mutane kusan 400,000 cikin haɗarin ambaliya da zaftarewar ƙasa, a cewar hukumar hana afkuwar bala’o’i ta yankin.

Kwamishinan hukumar Tesfaw Batable ya shaida wa gidan talabijin na Amhara TV da ke yankin, cewa gundumomi 32 na fuskantar ƙarin barazanar iftila’i saboda yawan ruwan sama da ake samu a yanzu.

Kazalika ya yi gargaɗin cewa lamarin na da matukar haɗari, musamman a yankunan Arewacin Gonder da Kudancin Gonder da kuma Wag Hemra, waɗanda a baya suka yi ta fama da ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Zaftarewar ƙasa ta yi ajalin aƙalla mutum 157

Ana ƙoƙarin shawo kan lamarin, amma fargabar haɗarin na ci gaba da tayar da hankula, a cewar kwamishinan.

Hukumomin yankin suna cikin shirin ko-ta-kwana bayan gargaɗin da cibiyar nazarin yanayi ta Habasha ta yi game da yiwuwar ƙarin zabtarewar ƙasa sakamakon ruwan sama da ake sa ran ci gaba da shatatawa nan gaba.

Wannan yanayi na damina da ake ciki ya matukar jefa yankuna daban-daban na ƙasar cikin haɗari, inda zabtarewar ƙasa ta shafi gundumomi da dama a yankin arewa da kuma kudancin Habasha.

A watan jiya, an fuskanci iftila’in zaftarewar ƙasa a jere a Gofa da ke yankin kudancin Habasha wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 260 tare da raba fiye da 15,000 da muhallansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here