Muna neman ƙarin jami’an tsaron domin fatattakar ‘yan bindiga a Shanono da Ɓagwai – Honarabul Badau
Daga Shafaatu Dauda Kano
Ɗan majalisa me wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono a Majalisar Wakilan Najeriya, Honarabul Yusif Badau, ya buƙaci ƙarin jami’an tsaro a mazabar tasa a sakamakon abin da ya kira hare-haren ‘yanfashin daji da ya addabi yankin.
Badau ya yi kiran ne ta cikin wani kudiri da ya gabatar a gaban zauren majalisar a yau Talata, inda ya lissafa lokutan da aka kai musu wasu hare-hare.
A cewar sa, “Yan bindigar sun fara kai hari ne wata kasuwa da ke garin Farin Ruwa a ƙaramar hukumar Shanono ranar 17 ga watan Afrilu, inda suka kashe mutum biyu, da raunata mutum shida baya ga sace mutum ɗaya”.
KU KUMA KARANTA: Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki – UNICEF
Haka kuma sun sake kai irin wannan hari a garin Shanono ranar 26 ga watan Afrilun, sai dai mutanen garin sun mayar musu da martani inda suka kore su.
Ya kara da cewa a ranar 2 ga watan Mayu ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutum daya a garin Fafarawa da Sandamu dake kananan hukumomin Shanono da Bagwai, harma suka sace wayoyi, da babura bakwai, sai dai ba’a sami asarar rai ba.
Tuni Majalisar ta aika batun ga kwamitin majalisar na tsaro da ‘yan sanda don daukar mataki na gaba.