Muna fatan ɗorewar zaman lafiya a jami’ar ABU Zariya – Farfesa Bala

0
146
Muna fatan ɗorewar zaman lafiya a jami'ar ABU Zariya - Farfesa Bala

Muna fatan ɗorewar zaman lafiya a jami’ar ABU Zariya – Farfesa Bala

Daga Idris Umar, Zariya

Mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Kabiru Bala, ya dauki zaman lafiyar da aka samu a jami’ar Ahmadu Bello Zariya a matsayin abin alfahari a lokacinsa kuma ya yabi takwaransa mai jiran gado, Farfesa Adamu Ahmed, da cewa mutumin kirki ne wanda ya ke shine sabon zabenben mataimakin shugaban Jami’ar a halin yanzu.

Farfesa Bala ya furta kalmar ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishin sa da ke jami’ar a Samaru.

Farfesa Bala ya ce, “Farfesa Ahmed mutumin kirki ne mai kwazo, na san shi da daɗewa yana da kokari sosai, mun yi mu’amula dashi sosai.

“Bisa saninsa ne na ke masa kyakkyawan fata tare da yi masa addu’a ta fara aiki lafiya da kammalawa lafiya.”

Bayan Farfesa Bala ya yi yabo da shaida ta gari ga takwaran nasa, Farfesa Ahmed, wanda shine zai karɓi jagorancin jami’ar a halin yanzun, Farfesa Bala ya kuma amsa wasu tambayoyi ga manema labarai akan wasu daga cikin nasarori da ya samu kasancewarsa shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Zariya a cikin shekaru biyar.

Farfesa Bala ya fara da godewa Allah tare da yabo na musamman ga dukkan bangarorin ilmi da lafiya da tsaro da shugabanin al’umma dake maƙotaka da jami’ar baki ɗaya.

Bayan haka Farfesa Bala ya dauki zaman lafiyar Jami’ar a matsayin abu na farko a ɓangaren nasara da ya samu a matsayin sa na shugaba a jami’ar.

Farfesan ya nuna cewa duk da ƙalubalen da harkar Ilimi ya fuskanta a lokacinsa hakan bai sanya sun rungume hannu ba wajan samo mafita a lamarin, ya ce a hakan suka dubi yadda zasu inganta jin daɗi da walwalar dalubai, inda ya sa aka gina ɗakuna masu yawan gaske a sashin Dan Fodio da bangaren dalubai masu koyan aikin lafiya a Asibitin koyarwa na Shika.

Read also:Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta yi bikin yaye ɗalibai kashi na 44

Shugaban ya tabbatar da samun tallafi mai tsoka na karatun ɗalubai daga bankin Opay.

Hakazalika shugaban ya nuna samun nasara akan harkokin motsa jiki tun daga gida Najeriya har zuwa ƙasashen waje, ya kuma sanar da Majalisar zartawar jami’ar ta amince da wani tsari na baiwa ɗalubai damar sake zana jarabawa wanda ɗalubai da dama sun amfana dashi, a ɓanagare ɗaya kuma suma jami’a sun sami sauki na rage yawan ɗaluban.

Yayin da shugaban yake bayyana wasu daga cikin kalubalen da ya fuskanta a kujerarsa, ya kawo tsaiko na rashin kuɗi da jami’ar ta fuskanta yayin annobar cutar korona, kuma shugaban ya bayyana wata shari’ar da jami’ar tasha kayi tare da biyan diyyar kuɗi masu yawan gaske da ya kai ga jami’ar ta faɗa cikin wahalar gaske da takai ga faɗawa cikin rigimar rashin wutar lantarki a kwanakin baya.

Karshe yayi jinjina ga mataimakin sa a ɓangaren ilmi da sauran jama’ar da suke tare dashi wanda da gudummuwarsu ne ya sami nasarar da jami’ar ta samu a karkashin sa.

Shugaban yayi jabo tare da godiya ga Allah da yasa har ya kawo yanzu bai sami tarzomar ɗalubai ba ballantana na ma’aikata.

Leave a Reply