Mun yi yarjejeniya da gwamnatin Katsina kan raya al’adu – Minista Hannatu Musawa
Daga Idris Umar, Zariya
Ministar harkokin raya al’adu da da ƙirkirarriyar basira wato Ministry of Art, Culture and Creative Economy, Barista Hannatu Musawa ta jagoranci sanya hannu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin jihar Katsina a fannin haɓaka al’adu da basira.
Kamar yadda Napetune Prime Hausa ta samu, an gudanar sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ɗakin taro na ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina a ranar Litinin.
Kwamishinan Ayyuka na musamman da cigaban tattalin arzikin al’ummar karkara, Farfesa Abdulhamid Ahmed Mani ne ya wakilci gwamnatin jihar Katsina a wurin rattaba hannu kan yarjejeniyar.
KU KUMA KARANTA:Gwamnan Lawal ya gana da ministan bunƙasa kiwon dabbobi
Da take jawabi, Barista Hannatu Musawa ta bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana da kyawawan tsare-tsare na haɓaka bangaren al’adu da kuma inganta rayuwar mutane ma su basira a fadin ƙasar nan.
Ta ƙara da cewa wannan yarjejeniyar za ta samar da cigaba sosai a jihar ta hanyar haɓaka tattalin arzikin jihar da al’ummar da ke cikin ta baki daya.
Shi ma da yake jawabi, Wakilin gwamnatin jihar Katsina kuma Kwamishina, Farfesa Abdulhamid Mani ya bayar da tabbacin goyon bayan gwamnatin jiha karkashin jagorancin Gwamna Mallam Dikko Umar Radda wajen tabbatar yarjejeniyar.
Daga bisani, tawagar Ministar ta je masarautar Daura da wasu wuraren tarihi da ke a fadin jihar da suka hada da Rijiyar Kusugu, Durbi Takusheyi da dai sauran su.