Mun samu kakin sojoji da maƙudan kuɗaɗe a gidan Mamu – DSS

0
451

Hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) ta ce ta ƙwato kayayyakin da suka haɗa da kakin sojoji da wasu maƙudan kuɗaɗe na ƙasashe daban-daban a gidan me shiga tsakanin masu garkuwa da kuma gwamnati, wato Tukur Mamu.

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani ga binciken jaridar Daily Trust game da wani samame da aka kai a gida da kuma ofishin Mamu da safiyar Alhamis a jihar Kaduna. Hukumar ta DSS ta ce abubuwa da dama da aka gano masu matuƙar tayar da hankali, inda ta ce za a gurfanar da mawallafin a kotu.

KU KUMA KARANTA: An kama Tukur Mamu, mai shiga tsakani don ceto fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Afunanya ya ce: “Ya zuwa yanzu, jami’an tsaro da suka dace sun aiwatar da sammacin bincike a gidan Mamu da ofishinsa. A yayin aikin, an ƙwato kayayyakin irin na masu laifi da suka hada da kayayyaki harda kaki na soja”.

“Sauran abubuwa sun haɗa da kuɗaɗe na ƙasashe masu yawa, da kuma na’urori na kayan mu’amalar kuɗi. Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, ya tabbata mamu seya amsa kira a kotu,” in ji Afunanya.

A wani labarin kuma, a daren ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne sojoji ɗauke da motoci ƙirar Hilux guda bakwai suka kai farmaki gidan surukin Mamu, wato Abdullahi Mashi dake Rigasa a Kaduna. Mamu, mai sasanta ‘yan fashin kwanan nan ya aurar da ‘yarsa ‘yar shekara 16, ga Abdullah Mashi. Yarinyar dalibar El-modern international school ce da ke Rigasa.

Leave a Reply