Mun amince hukuma ta duba fina-finan mu na YouTube kafin mu ɗora – Moppan
Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Fina-Finai ta Kasa reshen Kano (MOPPAN), Alhaji Ado Ahmed Gidan-Dabino yace ƙungiyar ta amince Hukumar Tace Fina-Finai Da Dab’i ta Jihar Kano ta dinga duba fina-finansu gabanin dorashi a shafin YouTube da sauran manhajoji.
Cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 22 ga Mayu, Gidan-Dabino yace wasu wakilan ƙungiyar sun zauna da shugabannin Hukumar Kuma sun cimma matsaya guda biyu.
Yace matsaya ta farko ita ce dole ne kowanne mashiryin fim ya mika aikinsa domin tacewa gabanin fitar da shi zuwa intanet.
KU KUMA KARANTA:Hukumar tace fina-finai ta kara soke lasisin wasu gidajen wasannin gala 8 tare da Haramta aikinsu na din-din-din a Jahar Kano
Matsaya ta biyu, a cewarsa, ita ce Hukumar Tace Finafinai Da Dab’i za ta samar da hanyoyin sauƙaƙawa mashirya Fina-Finai ta hanyar samar da tsarin mika fim ga Hukumar ta yanar gizo.
Gidan-Dabino ya bukaci abokan sana’arsa da su bayar da hadin kai ga Hukumar domin tsaftace harkar fim.