Mum shafe kwanaki 40 babu wutar lantarki – Mazauna lokon Maƙera ta jihar Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Al’ummar unguwar Lokon Makera dake karamar hukumar Gwale dake cikin kwaryar birnin Kano sun koka bisa yadda su ka shafe sama da kwanaki 40 ba tare da samun hasken wutar Lantarki ba.
A zantawar jaridar Neptune Prime da guda cikin Malaman Addinin musulunci a yankin Malam Muhammad Dauda lokon Makera, ya ce sun shiga wannan halin ne sakamakon lalacewar Injin da ke baiwa unguwarsu hasken wutar lantarki.
Malamin ya ce abin takaici ne yadda mutanen yankin su ke fama da matsalar wuta tun cikin Azumin watan Ramadan har zuwa yanzu kuma an kasa samun wanda zai warware musu matsalar cikin yan Siyasar dake karamar hukumar.
Malamin ya yi zargin nuna halin ko-in-kula daga shugabanni yankin musamman yan siyasa da su ka hada da Yan majalisar tarayya da takwaransa na majalisar dokokin Jihar Kano ya na mai cewa “mafi yawan al’umma ba su ma san wadanda ke wakiltarsu a yankin ba kuma cikinsu harda ni duk da kasancewata malamin Addinin musulunci kuma dan boko”.
KU KUMA KARANTA: Akwai barazanar katsewar wutar lantarki a faɗin Najeriya
” Mun rasa inda za mu sami dan majalisarmu na jihar da na tarayya ballantana mu kai musu kokenmu, don haka muna cigiyarsu su dubi Allah da ma’aiki su zo su cire mu daga wannan matsala”.
Dauda lokon Makera ya bukaci kamfanin rarraba hasken wutar Lantarki na jihohin Kano, Jigawa da Katsina KEDCO da ya kaiwa al’ummar yankin dauki.
Malamin ya ce matukar Yan siyasa a Gwale su ka gaza warware matsalolin da mutane ka fama da su akwai ranar kin dillanci, ranar da kwanne dan siyasa zai je da bukata kuma al’ummar su yi watsi da bukatarsa.