Muktar Adamu, ɗan shekara 4 da akayi garkuwa dashi a Potiskum ya samu ‘yanci

0
676

Wani yaro ɗan shekara 4 mai suna Muktar Adamu da ke unguwar Nahuta a ƙaramar hukumar Potiskum a jihar yobe, ya kubuta bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da shi a gidan mahaifinsa ranar Laraba.

An gudanar da aikin ceton kuɓutar dashi ne tare da goyon bayan al’umma da kuma jami’an tsaro a jihar. An kama masu garkuwa da mutanen ne a ranar Juma’a a unguwar Yindiski da ke ƙaramar hukumar Potiskum a jihar Yobe.

Mutane 4 da ake zargi da aikata wannan aika-aika sun yi daidai a hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike a garin Potiskum. Wani dan unguwar da bai so a bayyana sunansa ya ce tun da farko masu garkuwa da mutane sun shirya yin garkuwa da mahaifin dan shekara 4 Muktar (Mallam Adamu) cikin rashin sa’a shirinsu ya ci tura inda suka samu damar yin garkuwa da Muktar dan shekara 4.

Kokarin yin magana da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) rundunar ‘yan sandan jihar Yobe game da ƙarin bayani kan ci gaban case ɗin ya ci tura.

Leave a Reply