Miji ya ƙona matarsa mai juna biyu saboda ta ƙi amincewa da zubar da cikin

0
530

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Wata mata ‘yar ƙasar Lebanon mai ciki, Hana Mohammed Khodor ‘yar shekara 21 da mijinta ya yi mata mugun duka tare da cinna mata wuta ta mutu a asibiti.

Matar mai juna biyu na tsawon watanni biyar ta yi fama da ƙonewar ƙashi 100 bisa 100 na jikinta, ta mutu a ranar Laraba 17 ga watan Agusta, 2022, bayan shafe kwanaki 11 tana gwagwarmayar ceto rayuwarta a wani asibiti da ke arewacin Tripoli, birni na biyu mafi girma a ƙasar Lebanon.

Rahotanni sun bayyana cewa, mijin Khodor, mai suna A.A, ya banka mata wuta ne saboda ta ƙi zubar da cikin.

“Yarinyar ta mutu kuma sai da muka yi mata tiyata domin cire abun dake cikinta. An garzaya da Hana asibiti a cikin mawuyacin hali, inda jikinta ya ƙone sosai, bayan da mijinta ya banka mata wuta ta hanyar amfani da silindar gas din gidan.

“A.A. An ce ba ya son ƙarin haihuwa don guje wa matsalolin kuɗi. Ma’auratan suna da ‘ya’ya biyu”.

Wani likita daga Asibitin Al-Salam da ke Tripoli a baya ya faɗawa manema labarai cewa an kwantar da Khodor a ranar 6 ga Agusta.

Wani abokin iyalin, Abdul Rahman Haddad, ya shaida wa Labaran Larabawa cewa Jami’an tsaron cikin gida na Lebanon sun kama mijin, wanda ya yi niyyar ficewa daga ƙasar.

‘Yar uwar wacce aka kashe ta shaida wa gidan talabijin na yankin cewa A.A. ya lakaɗa wa matarsa ​​dukan tsiya domin ya tilasta mata zubar da cikin.

“Lokacin da ta ƙi zubar da cikin, sai ya dauke ta zuwa gida ya banka mata wuta ta amfani da silinda mai iskar gas,” in ji ta.

Kafin rasuwarta, dangin Khodor sun yi roko da yawa don neman tallafin kuɗi don taimakon biyan kuɗin jinyar ta a asibiti, wanda ya haɗa da ayyuka da yawa da ƙarin jini.

Leave a Reply