Messi ya jagoranci Argentina zuwa wasan ƙarshe na Copa America

0
90
Messi ya jagoranci Argentina zuwa wasan ƙarshe na Copa America

Messi ya jagoranci Argentina zuwa wasan ƙarshe na Copa America

Ɗan wasan gaba na Inter Miami Lionel Messi ya jagoranci ƙasarsa Argentina zuwa wasan ƙarshe na Copa America inda ta doke Canada da ci 2-0.

Messi mai shekaru 37 ya zura ƙwallo a minti shida da komawa daga hutun rabin lokaci.

Ɗan wasan Manchester City Julian Alvarez ne ya baiwa ƙasar wadda ke rike da kofin duniya damar samun wannan nasara bayan ƙwallon kusa da Rodrigo de Paul na Atletico Madrid ya buga.

Wannan dai shi ne karo na shida a karawa takwas da Argentina wacce ta lashe kofin Copa America sau 15 ta kai matakin wasan ƙarshe.

Wasan ƙarshen da Argentina za ta kara da Uruguay ko Colombia, zai kasance wasa na ƙarshe da Angel di Maria zai buga wa ƙasar kafin ya yi ritaya daga buga wasa sannan kuma akwai shakku kan makomar Messi.

”Za mu ji daɗin yanayin da muke ciki a matsayinmu na ƙasa kuma ƙungiya. Ba abu ba ne mai sauƙi kasancewarmu a matakin wasan ƙarshe domin sake fafatawa don zama zakara,” kamar yadda Messi ya shaida wa kafar TYC Sports.

Manajan Argentina Lionel Scaloni ya ce zai yi aiki don shawo kan Di Maria da Messi su ci gaba da buga wasannin ƙasa da ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Farin cikina ya dawo bayan komawa Inter Miami – Messi

“Yanayin Leo (Messi), yana kama da Angel,” in ji Scaloni.

”Dole ne mu bar shi ya yi abin da yake so, don ba za mu taɓa zama waɗanda za su rufe masa ƙofa ba, zai iya zama tare da tawagarmu har tsawon lokacin da yake so. kuma idan yana so ya yi ritaya kuma ya dawo ya kasancewa tare da mu, za mu yi farin cikin hakan.”

Jacob Shaffelburg, ɗan wasan ƙungiyar MLS Nashville ne ya ɓarar da mafi kyawun damar da Canada ta samu a farkon wasanta da Argentina.

Kasar Canada wacce ke matsayi na 48 a duniya, ta yi waje da ƙwallon da Alvarez ya zura a ragarta kana ya bai wa Argentina damar samun gurbi na gaba a wasan.

Duk da shan kayen Canada, tawagar ta yi rawar gani fiye da yadda ake zato a fafatawar da suka yi a gasar Copa America.

A ranar Lahadi ne tawagar Jesse Marsch wacce za ta ɗauki nauyin gasar cin kofin duniya ta 2026 tare da Mexico da Amurka, za su kara da wadanda suka sha kashi daga sauran wasan kusa da na ƙarshe a wasan neman matsayi na uku.