Me zai biyo bayan canza wasu kuɗaɗe a Nijeriya? Daga Ibraheem El-Tafseer

0
481

A ranar Laraba 26 ga watan Oktoban 2022 ne, Babban Bankin Nijeriya ya sanar cewa zai sauya fasalin takardun manyan kuɗin ƙasar daga Naira 200 zuwa sama.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ce za su yi hakan ne bisa buƙatar gwamnatin tarayya da kuma amincewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda matakin, zai shafi takardar naira 200 da naira 500 da kuma naira 1000.

Bankin ya ce za a yi wannan sauyi ne domin rage yawan kuɗin da ke yawo a hannun jama’a da rage hauhawar farashi da kuma magance yin jabunsu.

A dangane da hakan ne bankin ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.

Haka kuma CBN, ya ce sabbin kuɗaɗen da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022.

Ya ƙara bayani da cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗaɗen har nan da ranar 31 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2023.

A shekarar 2014 Babban Bankin ya sauya takardar naira 100 domin murnar cikar Nijeriyar shekara ɗari ɗaya da Turawan mulkin mallaka suka haɗe Kudanci da Arewacin ƙasar a 1914.

Sai dai wannan shiri na canza fasalin kuɗin, ya haifar da cece-kuce mai zafi a ƙasar. Wasu kuma suna ta tambayar, meye zai faru bayan wa’adin da babban bankin ya bayar ya ƙare?
Bayan wa’adin da bankin ya sa na 31 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2023, mutane ba za su iya amfani da tsofaffin takardun kuɗaɗen ba kuma.

A bayanan da bankin ya bayar ya ce, dukkanin bankunan da ke da waɗannan takardun kuɗi a yanzu suna iya fara mayar da su CBN ba tare da ɓata wani lokaci ba.
Gwamnan bankin ya ce, duk bankin da ya fara kaiwa shi za a fara bai wa sabbin takardun.

Ya shawarci jama’a masu mu’amula da bankuna waɗanda suke da kuɗaɗen a hannunsu da su fara kaiwa asusun ajiyarsu a bankunan domin a samu damar sauya su da wuri.

A sakamakon matakin ana sa ran dukkanin bankuna su bar cibiyoyinsu na tattara kuɗaɗe a buɗe daga Litinin zuwa Asabar, saboda wannan shi ne zai bayar da dama ga jama’a su mayar da kuɗaɗen a kan lokaci.

Domin hanzarta sauyin, Babban Bankin na Nijeriya ya dakatar da cajin kuɗin da ake biya na ajiye kuɗaɗe a bankuna.

Amma kuma sanarwar ta ce idan yawan kuɗin ya wuce ₦150,000 za a biya caji.

Da aka fara samun soke-soke da cewa babban bankin ƙasar bai bi ƙa’ida ba wajen yin canjin kuɗin a daidai wannan lokaci, sai
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce, ya bi doka da ƙa’ida wajen sauya fasalin takardun kuɗin ƙasar uku da yake shirin yi.

Kakakin CBN, Mista Osita Nwanisobi, na mayar da martani ne ga Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna Ahmed, wadda ta ce ba a tuntuɓi ma’aikatarta ba kafin aiwatar da sauyin.

Da take magana lokacin da ta bayyana a gaban wani kwamatin Majasliar Dattawa ranar Juma’a da ta gabata, Zainab ta soki shirin tana mai cewa “ba lokacin da ya dace ba ne”.

Sai dai Mista Nwanisobi ya ce hukumomin CBN sun bi ƙa’ida wajen neman amincewar Shugaba Buhari kamar yadda sashe na 2(b) da sashe na 18(a) da sashe na 19(a) (b) na dokar CBN ta 2007 suka tanada don neman sauya fasali da samarwa da fara aiki da kuma yaɗa sabbin takardun kuɗi na N200 da N500 da N1,000.

A ranar Laraba ne babban bankin ya ba da sanarwar sake takardun na naira, inda ya ce kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen ƙasar na hannun mutane maimakon bankunan kasuwanci.

CBN ya bai wa ‘yan ƙasar wa’adin kwana 47 da su mayar da kuɗaɗen ga bankunan kasuwanci kuma yana sa ran nan da 15 ga watan Disamba mai zuwa zai fitar da sabbin takardun N200 da N500 da N1,000 ɗin.

TARIHIN KUƊIN NIJERIYA

A shekarar 1880: Kuɗin farko na Nijeriya shi ne na Shillings (Sulai) da Pence (Kwabo). Tsabar kuɗin wanda Babban Bankin Ingila ya samar shi ne na Sulai ɗaya ( Kwabo 12) da 1 Penny wato Kwabo 1 da kuma 1/10, kuma bankin ‘yan kasuwa mai suna Bank for British West Africa shi ne yake rarraba kuɗin har zuwa shekarar 1912.

Daga shekarar 1912 zuwa 1959: Hukumar samar da kuɗaɗe ta Afirka ta Yamma (West African Currency Board (WACB), ta samar da takardun kuɗi da tsaba na farko ga ƙasashen Nijeriya da Ghana da Saliyo da kuma Gambia. Kuma babbar takardar kuɗi ta farko ita ce, ta fan ɗaya, yayin da sulai ɗaya shi ne tsabar farko babba a lokacin.

A shekarar 1959: Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya samar da takardun kuɗin ƙasar na farko, yayin da ƙasar ta daina amfani da takardar kuɗi da tsabar da bankin kasuwancin na haɗakar Afirka ta Yamma WACB yake samarwa.
A shekarar 1962: A wannan shekarar ne aka sauya yanayin kuɗin na Nijeriya, ya nuna matsayinta na mai cin gashin kanta saɓanin a baya, lokacin da take ƙarƙashin mulkin Turawan Birtaniya. An sauya Kuɗin da ke ɗauke da rubutun ’FEDERATION OF NIGERIA‘, zuwa wanda aka rubuta ‘FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA’, a sama.

A 1968: A wannan shekarar aka sake sauya takardar kuɗin saboda yadda aka saba amfani da su a lokacin yaƙin basasa.
A 1973: An sauya sunan kuɗin Nijeriya daga fan 1. An ɓullo da naira ɗaya wadda take daidai da sulai goma a matsayin babbar takardar kuɗin ƙasar. Yayin da ƙananan kuɗin da ake kira kwabo (kobo) guda ɗari ya zama naira ɗaya.

A 1977: A wannan shekara aka ɓullo da sabuwar takardar kuɗi ta naira Ashirin (₦20). A lokacin ta kasance takardar kuɗi mafi girma a ƙasar wadda Babban Bankin ya ɓullo da ita saboda bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar da kuma bai wa jama’a damar walwalar riƙe kuɗaɗe masu yawa ‘yan kaɗan maimakon tilin takarda. A karon farko an sa hoton wani fitaccen ɗan ƙasar a kan takardar kuɗin.

A shekarar 1979: An ɓullo da sabbin takardun kuɗi uku, na naira ɗaya da naira biyar da kuma naira goma (₦1, ₦5, ₦10). Domin mutane su iya ganewa tare da bambanta takardun an yi masu launi iri daban-daban. Sannan a bayan kowace takarda aka sanya hoton wasu abubuwa da ke nuna al’adun ƙasar.
A 1984: An sauya dukkanin launin takardun kuɗin in banda takardar kobo 50 a cewar hukuma domin shawo kan yadda ake ficewa da kuɗin ƙasar waje a lokacin.

A shekarar 1991: An sauya takardar kobo 50 da naira ɗaya zuwa tsaba.
A shekarar 1999: Domin abin da hukuma ta ce faɗaɗa harkokin tattalin arziƙin ƙasar da sauƙaƙa cinikayya, aka ɓullo da takardun kuɗi na naira ɗari ɗaya da naira ɗari biyu da naira ɗari biyar da kuma dubu ɗaya ( ₦100, ₦200, ₦500 da ₦1000) a watan Disamba na 1999 da Nuwamban 2000 da Afrilun 2001 da kuma Oktoban 2005.

A shekarar 2007: A matsayin wani ɓangare da sauye-sauyen tattalin arziƙi an ɓullo da takardar kuɗi ta naira Ashirin ta leda a karon farko. Yayin da kuma aka sauya fasalin zanen naira hamsin da naira goma da naira biyar har da naira ɗaya da kuma kobo hamsin, sannan aka ɓullo da tsaba ta kobo biyu.
A shekarar 2009: Sakamakon irin amfanin da gwamnati ta ce ta gani dangane da sauya takardar kuxɗin naira Ashirin zuwa ta leda, sai ta sauya naira hamsin da goma da kuma naira biyar zuwa na leda. A yanzu dukkanin ƙananan takardun kuɗin ƙasar na leda ne.

A shekarar 2010 da 2014: babban bankin ƙasar CBN, ya ɓullo da sabuwar takardar naira hamsin da ta naira ɗari domin bikin cikar Nijeriya shekara 50 da samun ‘yancin kai.

Leave a Reply