Me Yasa Matasa Suke Nuna Gazawar Su A Siyasar Najeriya?

0
354

Daga; Jabiru Hassan.

A DUK lokacin da aka yi magana kan matasa a wannan kasa tamu, nakan kara duba yadda matasan namu suka gaza tabuka komai a siyasar kasar nan tun lokaci mai tsawo.

Sannan kuma kowa ya amince cewa matasa sune kashin bayan samar da ci gaba a kowace kasa ta duniya duba da yadda zamani yake canzawa daga lokaci zuwa lokaci kamar yadda ake ciki a duniyar mu ta yau.

Haka Kuma tun da Najeriya ta koma kan tsarin mulkin farar hula watau a 1999, duk Dan takarar da zai yi yakin nemen zabe yana yin kirari da matasa, amma da zarar an ci zabe sai a mayar da matasan daga gefe.

Bugu da kari, ana yiwa matasa kirari da cewa sune Kan gaba wajen kawo sauyi domin suna da yawa, amma a karshe bayan an kammala zabuka sai a rika yi musu wayo da cewa za a basu horo kan sana’oi da jari domin dogaro dakai inda Kuma dan abin da za a bayar kankane.

Babbar matsala da matasan kasar nan ke ciki ita ce sun gaza tabuka wani abin kirki a harkar siyasar wannan kasa, musamman zaben 2023 inda dattawa suka babbake komai su kuwa matasa amfani kawai ake yi dasu domin cimma bukatu na siyasa da kuma mulki kamar dai yadda ake gani a yau.

Abin takaici shi ne matasan mu sun kware ne kawai wajen kakkafa kungiyoyin tallar yan takara domin samun abin duniya, wasu kuma sun kware wajen tayar da hargitsi lokutan zabe da sacewa ko farfasa akwatunan zabe da kuma hana zaben baki daya.

Wasu kuma sun kasance sai yawo gidajen masu mulki da Kuma iya rubuce-rubuce a kafafen sadarwa na zamani domin tallata gwanayen su
wanda hakan ta sanya yan siyasa manya da kananan su suka mayar da matasa gefe.

Masu cewa yanzu lokaci ne na a baiwa matasa mulkin kasarnan suna da Hujjojin su amma dai mafiya yawan al’umma basu san cewa matasa suna da manyan kalubalen dake dabaibaye shigar su fagen zabe ba wadanda suka hada da kwadayin samun abin duniya da kuma rashin iyayen gida a siyasar kasarnan.

Idan aka yi waiwaye kan yadda wadanda zasu shiga zaben 2023, ai matasan kadan ne suma kuma akwai manya a sama da suka daure masu gindi domin wata biyan bukata tasu da Kuma yin amfani dasu domin amfana da arzikin kasa cikin hikima.

Ina shawartar matasan kasar nan da su ci gaba da kasancewa masu kaunar zaman lafiya tare da neman arziki ta hanyoyi masu kyau. Sannan kada su bari yan siyasa su rika amfani dasu ana cin mutuncin al’umma ko Kuma tayar da hargitsi a wajen zabuka da dai sauran abubuwa da matasa suka kware akai.

A karshe, Yana dakyau matasa su tsaya suyi nazari domin zabar mutumin da zai kawo mafita garesu da kuma sanya su cikin madafun iko ta yadda zasu taka tsanin hawa Kan shugabanci wata rana wajen tafiyar da gwamnati a matakai daban-daban, tare da fatan samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano da Kuma kasa baki daya.

Jabiru Hassan, ya ruboto wannan makala daga Dungurawa Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.
(medialink57@yahoo.com)

Leave a Reply