Mayaƙan sa kai sun zakulo gawarwakin ‘yan boko haram sama da 100 da suka nutse a cikin ruwa

0
582

Mayaƙan sa kai sun bayyana cewa sun zaƙulo gawarwaki sama da 100 na ƴan Boko Haram ɗin daga cikin kogi inda suka binne su.

Gwamman mayaƙa masu iƙirarin jihadi na Ƙungiyar Boko Haram sun nutse a ruwa yayin da suke guduwa sakamakon luguden wuta ta sama da ƙasa da sojojin Najeriya ke yi musu a a jihar Borno.

Jami’an tsaron Najeriya sun ce sun kai hari ne a maɓoyar mayaƙan a can cikin dajin Sambisa.

Rahotanni sun ce baya ga farmakin sojojin, akwai ɗaruruwan mayaƙan da suka tsere tare da iyalansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye sansanoninsu.

Rahotanni sun ce ambaliyar da Kogin Yedzaram ya yi ne ya jawo ambaliyar da ta shafi sansanonin mayaƙan da dama, lamarin da ya ja suka yi hijira.

Dubban mutane ne dai suka mutu, kuma kusan mutum miliyan biyu ne mayaƙan na Boko Haram suka raba da muhallansu.

Sai dai a ƴan kwanakin nan jami’an tsaron ƙasar sun ce ana samun sauƙi sakamakon irn farmakin da suke kai wa mayaƙan. Haka kuma ana samun wasu daga cikin mayaƙan na Boko Haram da suke tuba suna miƙa wuta.

Kazalika wasu kuma sun bazama inda suke haɗewa da wasu ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadin irin su ISWAP da ta fi ƙarfi a arewa maso gabas da kuma ANSARU da ke da ƙarfi a arewa maso takiya da kuma wani fanni na arewa maso yammacin Najeriya.

Leave a Reply