Maulud: Gwamna Buni ya buƙaci al’umar musulmi kan addu’ar samun cigaban Najeriya

1
672

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, a ranar Asabar ya buƙaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da bikin Mauludi wajen yi wa Najeriya addu’o’in zaman lafiya da tsaro.

Buni wanda ya yi wannan kiran a cikin wani saƙo da ya aike wa al’ummar musulmi ta hannun Babban Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da manema labarai, Alhaji Mamman Mohammed a Damaturu, ya ce Idin Maulud bikin Musulunci ne na tunawa da Maulidin Annabi Muhammad (SAW).

“Ya kamata mu yi amfani da damar da wannan biki wajen yi wa jiharmu da kasarmu addu’ar samun haɗin kai da ci gaba.

“Hakazalika, yayin da muka fara shirin zaɓukan 2023, ina kira ga kowa da kowa da ya yi amfani da wannan damar don yin addu’ar yin zabe cikin lumana da nasara a 2023,” in ji Buni.

Ya ce an aiko Annabi Muhammad (SAW) ne ga bil’adama domin ya wa’azantar kan bautar Allah, tare da nuna aminci da kaunar juna.

Gwamnan ya hori Musulmi da su yi koyi da kyawawan ɗabi’un Manzon Allah da suka haɗa da gaskiya, da tawali’u, zaman lafiya da kaunar juna.

“Idan muka yi koyi da rayuwar Annabi Muhammad (SAW), duniya za ta zama mafi alheri ga kowa,” in ji Gwamna Buni.

Sai dai ya yi gargadin a guji yin amfani da wannan dama wajen shiga ayyukan da suka saɓa wa rayuwa da ɗabi’u da koyarwa da kuma ayyukan Manzon Allah.

Gwamnan ya yi wa kowa fatan alheri da zaman lafiya da tunawa da Mauludin.

1 COMMENT

Leave a Reply