Matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya – Amnesty

0
34
Matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya – Amnesty

Matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya – Amnesty

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen kare rayuka da dukiyar al’ummar ƙasar lamarin da ya sanya masu aikata laifi ke kai farmaki tare da hallaka al’umma.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a matsayin martani kan rahotanni kai hare-hare a jihar Zamfara, inda aka hallaka “mutane kimanin 20”.

A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙungiyar Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi ya yi zargin cewa akwai nakasu a dabarun da Najeriyar ke amfani da su wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar.

“Dabarun da gwamnati ke amfani da su wajen kare mutane na da rauni, kuma ya kamata a sake dabara,” in ji Sanusi.

KU KUMA KARANTA:‘Yansanda a Kano sun fitar da sabbin matakan tsaro a watan Azumi

Ya kuma yi zargin cewa a yanzu ƴan siyasar ƙasar sun mayar da hankali ne wajen tunkarar zaɓen shekara ta 2027 a maimakon kare rayuwar al’umma.

“Abin da ƴan siyasa suka mayar da hankali a kai shi ne ya za mu ci zaɓe?”

Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta fifita kyautata rayuwar mutane a maimakon siyasa.

Leave a Reply