Matashin da ‘Ƴandaba suka sare masa ƙafa ya nemi taimakon mahukunta

0
83
Matashin da ‘Ƴandaba suka sare masa ƙafa ya nemi taimakon mahukunta

Matashin da ‘Ƴandaba suka sare masa ƙafa ya nemi taimakon mahukunta

Daga Shafaatu Dauda Kano

Matashin nan mai suna Muh’d Abubakar Usman mazaunin unguwar Dorayi wanda ya rasa kafarsa guda daya sanadiyyar fadan daba da ya rutsa dashi.

Yau shekara daya da rabi kenan, yana kara rokon mahukunta da suyi masa adalci wajen bimasa hakkinsa akan zalincin da akai masa.

Muh’d yace, tun sanda wannan iftila’i ya fada masa suka kai batun gaban mahukunta. Cikin ikon Allah hukumar ta samu nasarar kama wasu daga cikin wadanda sukai wannan ta addancin.

Wanda hakan yasa muke tsammanin samun adalci game da zalincin da akaiwa wannan bawan Allah.

Sai dai har kawo yanzu Muh’d yace babu wani mataki gamsashshe da aka dauka akan wadan da suka shiga hannu.

KU KUMA KARANTA: Yan Daba sun shiga gidansu wani matashi sun kashe shi a Jihar Kano

A maimakon haka ma sai gashi wadanda ake zargin cutar da Muh’d sun fito daga hannun hukumar dake tuhumar tasun.

A lokacin dashi Muh’d ya rasa kafarsa guda daya an kassara masa rayuwarsa

A don hakane yake rokon duk wanda zai iya shiga cikin al’amarin domin bi masa hakkinsa da ya taimakeshi ya sanya hannu cikin maganar

Muh’d yace, bayan faruwar wannan al’amari iyayensa da ‘yan uwansa sun shiga cikin matsananciyar damuwa mara misaltuwa.

Leave a Reply