Matar gwamnan Zamfara ta ɗauki nauyin yi wa mata 100 aikin kansar mama

0
62
Matar gwamnan Zamfara ta ɗauki nauyin yi wa mata 100 aikin kansar mama

Matar gwamnan Zamfara ta ɗauki nauyin yi wa mata 100 aikin kansar mama

Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta ɗauki nauyin tantancewa da yi wa mata dari masu ɗauke da cutar kansar Nono tiyata kyauta a fadin jihar ta Zamfara.

Hajiya Huriyya ta bayyana hakan ne  a jiya Litinin yayin bikin tunawa da ranar mama ta duniya ta 2024 a jihar.

A jawabin ta ta bayyana cewa; ‘Yau ne ranar yaƙi da kansar Nono ta duniya don haka mu kabi sahu wajan tallafawa mata masu ɗauke da wannan cuta mai haɗari da ke jawo asara rayuka a Jihar mu.

KU KUMA KARANTA: Mawallafin Neptune Prime zai ƙaddamar da asibitin cutar kansa, makaranta, da gidauniyar tallafi a Yobe

Tare da goyon bayan maigidana gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, an tantance majinyata 100 da suka kamu da cutar kansar Nono za a yi musu aikin tiyata kyauta a jihar.

A kan haka muke ƙira ga waɗanda za a yi wa aikin da su bi dokar likitoci a lokacin jinyar don samun nasarar aikin da ɗorewar lafiyarsu.

Leave a Reply