Matar da mijinta ya ɗaure a ɗaki ta rasu a Kano

1
605

Daga Shafaatu Dauda, Kano

Sadiya, matar da mijinta ya daure ta a ɗaki tsawon watanni ta rasu a asibiti da aka kwantar da ita. A daren jiya ne ɗaya daga cikin masu jinyarta tare da taimaka mata, a ƙarƙashin Gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo Foundation, Musa Abdullahi Sufi ne ya sanar da rasuwar ta shafinsa na Facebook.

Ana zargin mijin marigayiyar ya kulle ta a ɗaki cikin tsananin rashin lafiya kuma bai kai ta asibiti ba, sai dai ya ba ta koko da naman hazbiya kamar yadda wata Majiya Ta shaida mana

Daga bisani mahifiyarta da ta kai mata ziyara inda take, da taga halin da ‘yar tata take ciki ta ɗaukota tadawo da ita asibitin Koyarwa na Malam Aminu kano AKTH. Kwanaki kaɗan da kawo ta Kano, mahaifinta ya rasu, sakamakon ganin halin da ‘yar tasa ta shiga cewar Abdullahi Sufi.

KU KUMA KARANTA:Yan sanda sun ceto yarinyar da ƙanwar mahaifiyarta ta kulle a Filato

Fitacceen dan gwagwarmayar ya ce ba za su kyale lamarin ba, sai sun ɗauki matakin da ya dace wajen bi wa marigayiyar haƙƙinta. Yanzu za mu duƙufa wajen nemo wa Sadiya haƙƙin ta wajen wannan miji da ya zalunce ta,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi hattara da wasu ƙungiyoyi da mutane ke neman tallafi da sunan marigayiya sadiyar.

Yadda mahaifiyar Saudiya ta sameta. An haɗa hoton da yadda Saudiya take lokacin tana gidansu kafin aure

1 COMMENT

Leave a Reply