Mata da ƙananan yara da dama sun mutu sakamakon fashewar Bom a Borno
Daga Ibraheem El-Tafseer
Fashewar wani Bom, wanda ake kyautata zaton ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka binne ya kashe mutane aƙalla takwas tare da jikkata wasu uku a ƙaramar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno. Majiya mai tushe ta ce fashewar ta auku ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Litinin lokacin da motocin da suka taso daga Rann hedikwatar ƙaramar hukumar Kala-Balge zuwa Gamboru Ngala suka yi karo da IEDS.
KU KUMA KARANTA:Matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya – Amnesty
Majiyar ta ce wurin da lamarin ya faru na kusa da Furunduma mai tazarar kilomita 11 daga Rann, inda suka ƙara da cewa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da mata da ƙananan yara. Wani jami’in rundunar haɗin gwiwa ta farar hula da ya yi magana a ɓoye ya tabbatar da cewa mutane takwas ne suka mutu a fashewar Bom ɗin. Wata majiya ta ce adadin waɗanda suka mutun zai iya haura takwas, idan aka yi la’akari da yawan mata da ƙananan yara da ke cikin motocin matafiyan.
Sojoji ko ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa dangane da fashewar Bom ɗin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.