Masarautar Gaya ta sauƙe Wazirin Gaya daga muƙaminsa
Daga Shafaatu Dauda Kano
Masarautar Gaya da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya, ta sauke Alhaji Usman Alhaji, daga Sarautar Wazirin na Gaya.
Masarautar ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwar Jami’in yada Labaran yankin Gaya, Munzali Muhammad Hausawa, ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a yammacin yau Laraba, inda aka bukaci al’umma da su dau wannan bayani da muhimmanci tare da daukar matakin da ya dace.
READ ALSO: Gwamnatin Tarayya zata haɗa hannu da Gwamnatin Jihar Kano domin gina cibiyar kasuwanci ta zamani
A wata wasika da aka aikewa tsohon mai rike da sarautar, wanda kuma shine tsohon Sakataren gwamnatin Kano a lokacin gwamnatin Ganduje, Masarautar ta bayyana cewa an janye sarautar ne saboda wasu dalilai da ba za a iya kauce musu ba, kuma matakin ya fara aiki nan take.
Haka kuma Sakataren Masarautar Gaya, Alhaji Bello Halilu, ya ce Masarautar na matukar godiya da irin gudunmawar da Alhaji Usman Alhaji, ya bayar da kuma jajircewarsa a lokacin da yake rike da mukamin Wazirin Gaya.
Sanarwar ta kara da cewa, Masarautar ta yaba da goyon bayan da Alhaji Usman Alhaji, ya baiwa harkokin masarauta da kuma kokarinsa wajen inganta al’adun gargajiya da tarihinta.
A ƙarshe sanarwar ta ce wannan mataki na nuna jajircewar Masarautar wajen kare mutunci, kimar sarauta da adana martabar tsarin gargajiya bisa ga al’ada da dabi’un da aka gada.