Maniyyata Hajji 3,155 ne sukai rijista a Kano

0
36
Maniyyata Hajji 3,155 ne sukai rijista a Kano

Maniyyata Hajji 3,155 ne sukai rijista a Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta kammala rijistar maniyyata 3,155 da za su gudanar da aikin Hajjin 2025.

Darakta hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbaffa ne ya sanar da hakan yayin karbar bakuncin tawagar Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Kasa a ofishinsa a ranar Alhamis.

Shugaban ya kuma bayyana irin shirye-shiryen da suke yi wa maniyyatan.

KU KUMA KARANTA:Allah ya yiwa fitaccen attajiri a Kano Alhaji Nasiru Ahali rasuwa

“An kammala shirye-shiryen da suka shafi takardu da jakunkunan hannu na maniyyatan yayin da ake ci gaba da kammala hada bizar su”. A cewar sa.

Alhaji Laminu ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa goyon bayan da take bai wa hukumar domin saukaka tafiyar da al’amuran Hajji.

A nata bangaren, Shugaban hukumar shige da fice na filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Aisha Shehu, ta ce ziyarar su na nufin karfafa hadin gwiwa don saukaka aikin Hajji.

Daga karshe sunyi fatan maniyyatan zasu sauka kasa mai tsarki lafiya, su kuma dawo lafiya.

Leave a Reply