Man o”War Ta Lere Ta Yi Taron Taya Mataimakin Kwamandan Kungiyar Na Jihar Kaduna Murnar

0
324

Daga; Isah Ahmed, Jos.

KUNGIYAR  tsaro ta Man o”War, reshen Karamar Hukumar Lere dake Jihar Kaduna, ta shirya taron taya tsohon  Kwamandan kungiyar, Suleiman Ahmed Rufa’i, murnar sabon matsayin da ya samu na mataimakin Kwamandan kungiyar na Jihar Kaduna, bangaren kudi da kididdiga, a garin Saminaka.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Karamar Hukuma Lere Alhaji Abubakar Buba, ya bayyana farin cikin Karamar Hukumar kan wannan sabon matsayi da wannan jami’i ya samu.

Ya ce babu shakka al’ummar Karamar Hukumar da Jihar Kaduna da kasa baki daya zasu  amfana da wannan matsayi, musamman ganin irin kokarin da kungiyar ta ke yi, wajen bayar da tsaro a kasar nan.

Shugaban wanda Mataimakinsa Mista Matthew Musa ya wakilta, ya yaba wa jami’an Kungiyar kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen tsaro a Karamar Hukumar.

A nasa jawabin Kwamandan Kungiyar ta Man o”War na Karamar Hukumar Lere,  M. A. Abubakar ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne, domin su karrama wannan shugaba nasu, tare da taya shi murna kan wannan sabon matsayi da ya samu.

 “Babu shakka wannan shugaba namu, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kafuwar wannan Kungiya a wannan Karamar Hukuma. Don haka muke ganin wannan karin girma da ya samu, namu ne gaba daya”.

Ya ce suna da jami’ai guda 140 a wannan yanki da suke gudanar da ayyukan tsaro a wurare daban daban. Don haka ya yi kira ga jama’a su cigaba da basu goyan baya da hadin kai, kan kokarin da suke yi, na yaki da bata gari a wannan yanki.

A nasa jawabin Sabon Mataimakin Kwamandan Kungiyar ta Man o” War na jihar Kaduna bangaren kudi da kididdiga, Sulaiman Ahmed Rufa’i, ya bayyana farin cikin sa kan yadda ‘yan Kungiyar, na Karamar Hukumar Lere suka shirya wannan taro.

Ya ce wannan taro zai dada karfafa masa karfin gwiwa kan wannan sabon matsayi da ya samu.

“babu shakka, ina daya daga cikin mutanen da suka fara shiga wannan Kungiya a wannan yanki shekaru 22, da suka gabata, har na kai ga rike  shugabancin ta.”

Ya yi kira ga al”ummar karamar Hukumar, su cigaba da basu goyon baya ta hanyar turo matasan su zuwa wannan kungiya, musamman a wannan lokaci na matsalar rashin tsaro, domin su bada gudunmawarsu.

Shugabannin tsaro na wannan yanki, da suka da ‘Yan sanda da Jami’an tsaron farin kaya da Jami’an shige da fice da Jami’an kiyaye hadura da Jami’an Hukumar gyara hali, da suka halarci wajen wannan taro, sun yi jawabai na nuna murna tare da jawo hankali jama’a kan mahimmancin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here