Mahukunta sun kama mutumin da ya tafi Makka takanas don yi wa Sarauniya Umara

0
285

Mahukunta a Saudiyya sun kama wani mutum wanda ya tafi Makka takanas don yin Umara a madadin Sarauniya Elizbeth ta II.

A ranar Litinin ne mutumin, wanda ɗan asalin ƙasar Yemen ne ya wallafa bidiyonsa a babban masallacin Makka yana ɗawafi.

A cikin bidiyon ya rubuta cewa na sadaukar da Umarar da na yi ga Sarauniya Elizebeth ta II, ya ce yana addu’ar Allah Ya yafe mata kura-kuranta.

An dai yaɗa bidiyon a kafafan sada zumuntar Saudiyya inda mutane suka rinka kira a shafukansu na Tiwita da a kama shi.

Saudiyya ta haramta wa mahajjatan da suke je ƙasar daukar kwalaye mai dauke da rubuce-rubuce ko kuma ambatar sunan wasu da zummar kamfen ko wani abu dabam.

Yayin da aka amince cewa wani zai iya yi wa mamaci Musulmi Umrah, ba a amince a yi wa wanda ba Musulmi ba kamar Sarauniya, wadda shugaba ce a Cocin Majami’ar Ingila.

Leave a Reply