Maharan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna sun sako wasu fasinjoji 7 da suka sace

0
445

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Bakwai daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin da aka kai kan jirgin ƙasa a jihar Kaduna ranar 28 ga Maris, sun sami ‘yanci.

An sako mutanen bakwai ne a safiyar Laraba bayan da suka shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan.

Tukur Mamu, mawallafin Desert Herald, wanda ya shiga tattaunawar ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa shida daga cikin waɗanda aka sako ‘yan gida ɗaya ne amma har yanzu hukumomin ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

Sai dai ba a bayyana ko an biya kuɗin fansa ga ‘yan ta’addar domin a sako su ba.

A cewar gidan talabijin na Channels, sunayen mutanen shida Abubakar Idris Garba, uban yara hudu; matarsa, Maryama Abubakar Bobbo, da babban ɗansu, Ibrahim Abubakar Garba mai shekaru 10.

Sauran sun haɗa da Fatima Abubakar Garba mai shekaru bakwai; Imran Abubakar Garba ɗan shekara biyar da Zainab Abubakar Garba mai shekara daya da rabi kacal.

Abubakar dai ɗa ne ga Chris Garba, tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Kano da Benue.

Maharan sun kuma sako wata mata mai suna Aisha Hassan mai shekaru 60 da haihuwa, wacce ke fama da matsalar lafiya a lokacin da take tsare.

Idan ba a manta ba a ranar 28 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu fasinjoji yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama.

Tun da farko dai ‘yan ta’addan sun buƙaci naira miliyan 100 kafin a sako waɗanda suka mutun kamar yadda wasu ‘yan uwa na waɗanda abin ya shafa suka bayyana.

A kwanakin baya ‘yan ta’addan sun sako wasu mutane biyar da fasinjojin suka yi garkuwa da su.

Waɗanda aka ceto sun hada da Farfesa Mustapha Umar Imam, wanda likita ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.

Ya zuwa yanzu, daga watan Yuni zuwa yau fasinjojin kasa da kasa 22 ne suka samu ‘yancinsu.

Leave a Reply