Mahaifi da ɗan sa sun rasa rayukansu sakamakon faɗawa riijiya da sukayi a jihar Kano

0
490

Daga Shafa’atu DAUDA, Kano

Wani Magidanci ɗan shekara 60, Malam Bala tare da ɗansa, Sunusi Bala, mai shekaru 33 sun faɗa wata tsohowar rijiya da ke Sabon garin Bauchi, a ƙaramar hukumar Wudil, da ke cikin jihar Kano, inda suka rasa rayukansu kafin a kai ga cetosu.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da mutuwar ta su, yau laraba a Kano, inda ya ce uba da ɗan nasa sun rasu ne ya yin da suke ɗiban ruwa a rijiyar.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata da safe.

“mun sami kiran gaggawa daga ofishin hukumar kashe gobara na Wudil, da misalin ƙarfe 11: 30 na safe, cewa uba da ɗan sa sun fada rijiya”

“Nan take muka tura jami’an mu domin cetosu”

Sanarwar ta tabbatar da cewa an sami nasarar fito dasu daga rijiyar, amma jim kaɗan bayan fito da su, suka ce ga garin kun nan.

Leave a Reply