Magidanci a Kano, ya sha da ƙyar a hannun kan zargin ƙwacen waya
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Wani Magidanci ya sha daker a hannun matasa sakamakon zargin sa da Kwacen wayar wata mata.
Lamarin ya faru cikin daren Talata, a unguwar Gaida dake yankin karamar hukumar Kumbotso a Kano,
Matar ta shaidawa Jaridar Neptune Prime cewar, tana cikin tafiya cikin dare bayan sallah Isha’i tana waya, kawai sai ji ta yi anfizge mata waya, a lokacin da ta jiyo sai wanda ya fizge wayar ya zare mata wuka, domin tsorata ta.
Shi ne ta yi shiru, bayan ya fita da gudu ne kuma, sai ta sanya masa ihun “barawo” nan da nan jama’a suka tare shi suka fara dokan sa.
Kafin ayi wata-wata wannan mutumi, matasa sun yi masa jina-jina, kamar yadda wani matashi mai suna Aminu shima ya bayyana, kuma yana daya daga cikin wanda yasanya hannu ya daki wanda ake zargin da kwatar waya.
KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar ‘Take It Back Movement’ ta yi zanga-zangar tsadar rayuwa
“Na dake shi ne sabida nima kwanakin baya haka wasu barayin waya suka zaremin wuka suka kwacemin waya, inaji inagani haka na hakura domin tsira da raina da lafiya sa, hakan yasa nima na wuce fushin na akan wannan mutumi”. A cewar sa.
Sai dai bayan wanda ake zargin ya jigata ne, Jaridar Neptune Prime ta tambayi wanda ake zargin da fashin wayar sai yace “tsotsayi ne, wallahi shi baitaba aikata sata ba, tsautsayi ne yasa ya aikata, sabida kuncin rayuwa na babu, ga iyali ya fita baisamu abinda zai bawa iyalansa ba, shiyasa ya fito domin ya samo musu abinda zasuci”
A nan take aka saki mutumin ba tare da mika shi wajen jami’an tsaro ba, kuma wasu daga cikin al’umma suka fara hada masa kudi domin ya je ya yi wa iyalansa cefa ne suci abinci.