Ma’aikaciyar Shari’a, mai kare haƙƙin dan adam, taci zarafin ‘yar sanda a Abuja

1
875

Sifeta Janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya Usman Alƙali Baba ya yi tir da cin zarafin wata ‘yar sanda da uwargidanta ta yi.

An zargi Farfesa Zainab Duke Abiola da cin zarafin sifeta Teju Moses, saboda ta ƙi amincewa ta yi mata ayyukan da ba su shafi waɗanda aka dauke ta aiki ta yi ba daga hukumar ‘yan sanda.

KU ƘALLI BIDIYON ANAN: https://youtu.be/2UykT6JqPmc

Teju na aiki ne da Farfesa Zainab, wadda ma’aikaciyar shari’a ce kuma mai yaƙin kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya, a matsayin odali.

Kuma lamarin ya faru ne a gidan Farfesar da ke anguwar Garki da ke Abuja ranar 20 ga watan Satumba.

Yanzu haka Farfesa Zainab da wasu yaran gidanta da ake zargi da hannu a cin zarafin na hannun rundunar ‘yan sanda inda ake ci gaba da bincike.

Kazalika IGP Usman Alkali ya umurci a janye duka yan sandan da ke aiki da Farfesar.

Ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda matar da ke iƙirarin kare haƙƙin bil adama za ta ci zarafin wani mutum, musamman wadda aka nadya don ta ba ta kariya.

Kwanan nan ne rundunar yan sandan Najeriyar ta ba da sanarwar ɗaukar matakin doka, ga duk wanda ya ci zarafin ɗan sanda ta ko wace siga.

1 COMMENT

Leave a Reply