Liverpool ta doke Ajax 2-1, taci wasan farko a Champions League na bana

0
245

Liverpool ta yi nasarar doke Ajax da ci 2-1 a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League da suka fafata a Anfield ranar Talata.

Mohamed Salah ne ya fara ci wa Liverpool kwallo a minti na 17 da take leda, minti 10 tsakani Ajax ta farke ta hannun Mohammed Kudus.

Joel Matip ne ya ci wa Liverpool kwallo na biyu da ya bai wa kungiyar damar lashe wasan farko a kakar bana a Champions League.

Daman Jurgen Klopp ya bukaci ‘yan wasa da su saka kaimi, bayan da Napoli ta doke Liverpool 4-1 a wasan farko a rukunin farko a makon jiya.

Liverpool ta samu damarmaki da yawa, shi ne har ta kai kungiyar Anfield ta ci kwallon farko.Ita kanta Ajax, wadda ta doke Rangers 4-0 a makon jiya ta zubar da damarmaki da yawa.

Leave a Reply