Kyaftin ɗin wasan ƙwallon ƙafa ta Najeriya Ahmed Musa ya auri mata ta 4 a Kano

0
108
Kyaftin ɗin wasan ƙwallon ƙafa ta Najeriya Ahmed Musa ya auri mata ta 4 a Kano

Kyaftin ɗin wasan ƙwallon ƙafa ta Najeriya Ahmed Musa ya auri mata ta 4 a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tauraron ƙungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya ɗaura aure da matarsa ta hudu, Asmau Moriki, a wani biki da aka gudanar a asirce a Jihar Kano.

Sabon auren na zuwa ne bayan wasu shekarun da dangantakar aurensa ta baya ta janyo ce-ce-ku-ce a kafafen watsa labarai.

Auren farko na Ahmed Musa ya kasance da Jamila a shekarar 2013, wanda suka haifi yara biyu, sai dai auren ya mutu a shekarar 2017 bayan samun saɓani da rahotanni suka danganta da niyyarsa ta ƙara aure.

KU KUMA KARANTA:An je saka rana, sai kawai aka ɗaura aure – Amarya A’isha Humaira

Bayan rabuwa da Jamila, Ahmed ya auri Juliet Ejue daga Ogoja a Jihar Cross River a matsayin mata ta biyu, wannan auren ma ya zo ƙarshe, ko da yake ba a bayyana cikakken lokacin da suka rabu ba.

A shekarar 2021, Ahmed Musa ya ƙara aure da Mariam, wacce ta zama matarsa ta uku.

Yanzu a shekarar 2025, Ahmed Musa ya ƙara ɗaura aure da Asmau Moriki, wanda hakan ya sanya mata huɗu a cikin gidansa. Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da auren ne a sirrance, inda iyalai da ƙawaye na kusa da su ne kawai suka halarta

Leave a Reply