Kwankwaso da Ganduje ku haƙura da rikicin siyasar nan haka domin ci gaban Kano – Kashim Shettima

0
138
Kwankwaso da Ganduje ku haƙura da rikicin siyasar nan haka domin ci gaban Kano - Kashim Shettima

Kwankwaso da Ganduje ku haƙura da rikicin siyasar nan haka domin ci gaban Kano – Kashim Shettima

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya roƙi ‘yan siyasar jihar Kano da su tuna irin zumuncin da ke tsakaninsu ka da su bari bambancin ra’ayin siyasa ya raba kansu.

Kashim Shettima ya yi wannan roƙo ne a gaban gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da Shugaban jam’iyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas da sauran jiga jigan yan siyasa daga bangaren Kwankwasiyya da Gandujiyya, a lokacin da yake ta’aziyar rasuwar Galadiman Kano marigayi Abbas Sunusi.

Kashim Shettima ya ce kuskure ne shiyasa a jiha kamar kano da ake takama da ita a kowanne mataki ta raba kan mutanan Kano ko kawo cikas a tsakaninsu.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta kori ƙarar Kwankwaso da ke ƙalubalantar shugabancin NNPP

“Jihar Kano itace abar koyi a duk Najeriya, dan haka bama murna idan munga ana samun sabanin ra’ayin siyasa kuma ana nuna juna yatsa. Kano itace cibiyar Arewa, duk abinda ya shafi Kano ya shafi Arewa.

“Wannan tasa na ke fadar wannan sako da harshen Hausa, duk dacewa ni ba cikakken bahaushe bane, amma na kokarta na fada muku wannan sako da hausa ne domin ku fahimta sosai,” a cewar Kashim Shettima

Yayi fatan Allah yaki kan marigayi Galadiman Kano yasa yana Aljanna.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma jajantawa iyalan wadanda akayi garkuwa da dan ruwansu a Shanono da wadanda suka rasa rayukansu lokacin harin da yan bindiga suka kai yankin.

“Muna rokon Allah ya bamu zaman lafiya a Najeriya da kasa baki daya,”Inji Kashim.

Leave a Reply