Kotun Soji a Najeriya ta yanke wa wani soja hukuncin kisa

0
74
Kotun Soji a Najeriya ta yanke wa wani soja hukuncin kisa

Kotun Soji a Najeriya ta yanke wa wani soja hukuncin kisa

Daga Shafaatu Dauda Kano

Wata kotun soji a Nijeriya ta yanka wa wani soja mai muƙamin kurtu, Adamu Mohammed, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe budurwarsa.

‎Kwamandan batalita ta 82 ta rundunar sojin Nijeriya Manjo-Janar Oluyemi Olatoye, ne ya ƙaddamar da kotun sojin mai alƙalai 11 a watan Fabrairu shekarar 2025 domin hukunta sojoji masu laifi a rundunar.

‎Wata sanarwa da muƙaddashin mataimakin mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Jonah Unuakhalu ya fitar ta ce kotun ta samu jagorancin Birgediya Janar Sadisu Buhari.

KU KUMA KARANTA:Mulkin soja ya fi mana alheri a kan Dimokuraɗiyya – ‘Yan Nijar Mazauna Najeriya

‎“Shugaban kotun, Birgediya Janar Sadisu Buhari, a lokacin da yake yanke hukunci kan wanda ake tuhuma, Adamu Mohammed, ya bayyan cewa an same shi da laifin kashe budurwarsa, Hauwa Ali, laifin da ake iya hukuntawa a ƙarƙashin sashi na 106 (a) na dokar sojin Nijeriya ta shekarar 2004,” in ji sanarwar.

‎Ta ƙara da cewa alƙalan kotun dukka sun sami sojin da laifi ne bayan sun yi nazari kan hujjojin da aka gabatar a gabansu da bayanan tarihin aikin sojan tare da la’akari da afuwar da wanda ake tuhuma da lauyansa suka nema.

‎Sai dai kuma kotun ta ce dole a aiwatar da hukunci mafi tsauri domin yi wa wadda aka kashen adalci da kuma tabbatar da doka da oda.

Leave a Reply