Kotun Masana’antu ta Ƙasa ta umarci ASUU da ta janye yajin aikin watanni 7

1
735

Kotun kolin masana’antu ta ƙasa ta umarci kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), da ta janye yajin aikin da ta shiga. Ku tuna, yajin aikin ASUU na sama da watanni bakwai wanda ya hana ayyukan ilimi a makarantun gwamnati, ya fara a ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

Ƙungiyar na buƙatar a saki kuɗaɗen farfado da jami’o’i, a sake tattaunawa kan yarjejeniyar FGN/ASUU na shekarar 2009, a saki kuɗaɗen alawus-alawus na malaman jami’o’i, da kuma fara amfani da manhajar jami’o’i ta ‘Transparency and Accountability Solution’ (UTAS).

A bisa ƙarar da gwamnatin ta shigar, Justice Polycarp Hamman ya hana ASUU ci gaba da yajin aikin har sai an yanke hukunci. Gwamnatin ta yi ikirarin cewa ta magance mafi yawan buƙatun ƙungiyar da suka haɗa da fitar da N50b domin biyan alawus-alawus na albashin ma’aikatan jami’o’i masu koyarwa, da na waɗanda ba masu koyarwa ba, amma ta ce ba za a biya ƙungiyar albashinta ba na lokacin da sukayi Yajin aiki.

Kungiyar ta ASUU ta kuma dage kan cewa ba za ta janye yajin aikin ba har sai an warware basussukan da suke bi. Biyo bayan dagewar da ASUU ta yi na cewa ba za ta koma ba, gwamnatin tarayya ta hannun ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ta maka malaman jami’o’in da ke yajin aiki a gaban kotun masana’antu ta kasa (NIC).

Amma da yake yanke hukunci a kan umarnin shiga tsakanin da gwamnati ta shigar, a ranar Laraba, 21 ga Satumba, 2022, Mai shari’a Polycarp Hamman ya hana ASUU ci gaba da ɗaukar matakin masana’antu har sai an yanke hukunci.

Mai shari’a Polycap wanda alkali ne na hutu ya bayar da umarnin a mayar da ƙarar da aka shigar ga shugaban kotun masana’antu domin mayar da qarar ga wani alkali.

1 COMMENT

Leave a Reply