Kotun Ɗaukaka ƙara ta Najeriya ta umarci ASUU ta koma aiki ba ɓata lokaci

0
532

Kotun Ɗaukaka kara ta Najeriya ta umarci Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasar, ASUU da ta gaggauta komawa bakin aiki ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Hukuncin ya biyo bayan ɗaukaka ƙarar da ƙungiyar ta yi ne a kan hukuncin da Kotun Ƙwadago ta ƙasar ta yi ne inda ta umarci ƙungiyar ta ASSU da ta kawo karshen yajin aikin da ta kwashe wata takwas tana yi.

Sakamakon kasa warware dambarwar da ke tsakanin ɓangarorin biyu ne, gwamnatin Najeriya ta gurfanar da ƙungiyar malaman jami’o’in a gaban Kotun Ƙwadagon.

Daga nan ne ita kuma Kotun Ƙwadagon a ranar 21 ga watan Satumba ta umarci ƙungiyar da ta koma bakin aiki ba tare da ɓata wani lokaci ba, kafin a kai ga warware saɓanin da ke tsakaninsu da gwamnati.

Kotun ɗaukaka karar ta shawarci bangarorin biyu da su je su sasanta rikicin a wajen kotu, amma kuma abin ya ƙi yuwuwa, kamar yadda babban lauyan da ke wakiltar ASUU Femi Falana (SAN), ya sheda wa kotun yayin zamanta a Abuja, a jiya Alhamis.

Haka shi ma lauyan ɓangaren gwamnati a shari’ar James Igwe ya shaida wa kotun cewa sasanton a waje ya gagara.

A hukuncin da ya yanke yau Juma’a alkalin Kotun Ɗaukaka ƙarar Justice Hamman Barka ya umarci ƙungiyar malaman da ta koma aiki ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Ita dai ASUU tana yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu, inda mambobinta wato malaman jami’o’in gwamnati suka dakatar da aiki a kan kin biyansu kudaden alawus-alawus tare da neman kyautata jin dadinsu da sauran bukatu daga gwamnatin tarayya.

Gwamatin Najeriya ta yi wa wasu sabbin ƙungiyoyi biyu na malaman jami’a da suka ɓullo waɗanda ke zaman tamkar kishiya ga ASUU.

Ƙungiyoyin su ne CONUA da NAMDA ( Congress of Nigerian Universities Academics) da (National Association of Medical and Dental Academics).

Kuma ASUU ta ce za ta kai gwamnati ƙara kan yi wa ƙungiyoyin biyu rijista.

Leave a Reply