Kotu tayi watsi da hukuncin zaɓen ƙananun hukumomin jihar Kano

0
62
Kotu tayi watsi da hukuncin zaɓen ƙananun hukumomin jihar Kano

Kotu tayi watsi da hukuncin zaɓen ƙananun hukumomin jihar Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Kotun ɗaukaka kara dake Abuja, ta rushe hukuncin da babbar kotun tarayya dake jihar Kano ta yanke akan zaben kananan Hukumomin Kano.

Idan za’a iya tunawa jam’iyyar APC reshen jihar Kano da wasu mutane ne suka shigar da kara tare da neman a dakatar da zaɓen ƙananun hukumomin, daya gudana a shekarar data gabata saboda zargin cewa shugaban hukumar zabe ta jihar mamba ne a jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matashin da ya kona masallata a Kano

Sai dai a yau Juma’a mai sharia Oyewumi, na kotun daukaka kara ya ce tun da farko babbar kotun tarayya bata da hurumin sauraron ƙarar ballantana ta yi hukunci akai.

Akan wannan hujja kotun ta amince da bukatar bangaren gwamnatin Kano, wajen yin watsi da hukuncin kotun baya

Leave a Reply