Kotu ta ɗaure mutum shekara 30 a gidan yari saboda ya zagi sarki a facebook

0
596

Kotun Soji a ƙasar Thailand ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin shekaru 30 a gidan yari saboda ya wallafa hoto da wasu kalaman ɓatanci akan Sarkin Bhumibol Abulyadej, sarki mai shekaru 87 da ke da cikakkar kariya daga ɓatanci ƙarƙashin dokar Thailand, kuma duk wani da aka kama ya zagi Sarki ko Sarauniya ko ‘yan gidan sarautar ƙasar zai fuskanci hukuncin ɗaurin shekaru 15 ga duk ɓatanci da ya aikata ga daya ɗaga cikinsu.

Kotun ta ce ta kama mutumin mai suna Pongsak Sriboonpeng, mai shekaru 48 da laifin wallafa hotuna da saƙo sau shida a Intanet. Akan haka aka yanke masa hukunci ga duk saƙon da ya wallafa.

A tsarin Dokar ƙasar Thailand mutum bai iya ɗaukaka ƙara idan Kotun Soji ta yanke hukunci a kansa, kamar yadda lauyan da ke kare Sriboonpeng ya shaida.

A ranar alhamis ma kotun ta kama wani da laifin lalata hoton Sarki da Sarauniyarsa.

Wannan hukuncin dai na daga cikin mafi tsauri da mahukuntan Sojin Thailand suka zartar tun bayan da suka kwace mulki a shekarar 2014.

Leave a Reply