Kotu a osun ta yanke wa wani Malami hukuncin kisa ta hanyar rataya

0
45
Kotu a Kano ta yanke wa wani Malami hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu a osun ta yanke wa wani Malami hukuncin kisa ta hanyar rataya

Daga Shafaatu Dauda Kano

Wata kotu mai zamanta a garin Iwo, cikin jihar Osun, ta yanke wa wani malamin tsibbu mai suna Kabiru Ibrahim hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa samun sa da laifin kisan wani matashi almajirinsa, Lukman Adeleke.

Alkalin kotun, Justice Lateef Adegoke, ne ya yanke hukuncin bayan kotu ta tabbatar da cewa Kabiru ya aikata laifin tare da hujjoji gamsassu daga masu shigar da ƙara. Laifukan da aka tuhume shi da su sun haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, kisan kai, da kuma sata

KU KUMA KARANTA: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matashin da ya kona masallata a Kano

Justice Adegoke ya bayyana cewa Kabiru Ibrahim zai yi zaman gidan yari na tsawon shekaru bakwai kan laifin sata, kafin daga bisani a aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kisan kai.

Wata sanarwa daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Osun ta bayyana cewa marigayin Lukman Adeleke almajiri ne karkashin kulawar Kabiru Ibrahim. Sanarwar ta ce Kabiru ya shaidawa Adeleke cewa yana da wata filin saye, inda ya bukaci ya zo da dare da kuɗi domin a yi addu’a kafin a kammala sayen filin.

Bayan tafiyar Adeleke wajen malamin da dare, ya ɓace babu wani labari. Hakan ne ya tilasta iyalansa kai ƙara ga hukumar ‘yan sanda.

A yayin bincike, Kabiru ya amsa laifin kashe Adeleke, sannan ya jagoranci jami’an tsaro zuwa inda ya binne gawar marigayin, wato gefen babban titin Ilesa zuwa Akure, inda aka gano gawar a cikin buhu.

Leave a Reply