Kotu a Kano ta yanke wa matashin da ake zargi da cinnawa budurwarsa wuta ɗaurin shekaru 15

0
133
Kotu a Kano ta yanke wa matashin da ake zargi da cinnawa budurwarsa wuta ɗaurin shekaru 15

Kotu a Kano ta yanke wa matashin da ake zargi da cinnawa budurwarsa wuta ɗaurin shekaru 15

Daga Jameel Lawan Yakasai

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 1 ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Dije Abdu Aboki ta yanke wa wani matashi daga ƙaramar hukumar Takai hukuncin daurin shekaru 15 a gidan gyaran hali, bisa laifin yunkurin kisan kai ta hanyar cinnawa budurwarsa wuta.

An gurfanar da matashin mai suna Abdullahi Saidu, ɗan asalin garin Sakwaya da ke ƙaramar hukumar Takai, bisa zargin cinnawa budurwarsa Sa’adatu Ibrahim wuta saboda an dawo masa da kayan auren da ya kamata.

Kotun ta saurari shaidu uku daga masu gabatar da ƙara kuma lauyoyin gwamnati Barista Hajara Ado Sale da Barista Sadiya Sambo da kuma shaida ɗaya daga ɓangaren wanda ake ƙara.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Kano ta tura Mutane 29 da ake zargi da Kashe DPOn Rano gidan Yari

Bayan nazarin shari’ar, kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 15, tare da umarnin ya biya diyyar Naira miliyan ɗaya ga wadda abin ya shafa, ko kuma ƙara shafe shekaru 5 a gidan yari idan ya kasa biyan kudin.

Bayan zaman kotu, Barista Hajara Ado Sale ta ce hukuncin ya dace da nauyin laifin, yayin da lauyoyin wanda aka yanke wa hukunci suka ƙi cewa komai ga manema labarai.

Leave a Reply