Kotu a Kano ta bada umarnin cigaba da tsare fitaccen dilalin Migayun Kwayoyi Suleiman Dan Wawu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wani fitaccen mai sayar da miyagunkwayoyi, Sulaiman Aminu, wanda aka fi sani da Danwawu.
Alkalin kotun, M.S. Shu’aibu, ya bayar da wannan umarni, bayan Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gurfanar da wanda ake zargin.
KU KUMA KARANTA:‘Yan sanda sun kama dillalin ƙwaya a Kano, sun ƙwace tramadol ta naira milyan 25
Wata sanarwa da kakakin hukumar NDLEA ta jihar Kano Sadiq Maigatari ya fitar, ta ce an kama wanda ake zargin ne a wani samame da rundunar ‘yan sandan Kano ta kai gidansa, inda daga bisani aka mika shi ga hukumar ta NDLEA domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da shi gaban kotu
Mai Shari’a M.S. Shu’aibu ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Yuni mai zuwa.