Ko me ke janyo shanyewar ƙafa ga uwa bayan haihuwa?

0
253

Daga cikin matsalolin da iyaye mata ke fuskanta yayin naƙuda wadda ke hana su tafiya bayan haihuwa saboda raunin ƙafafu akwai matsalar nan da ake cewa “Maternal Obstetric Palsy” a turancin likita.

Wannan matsala na faruwa ne yayin naƙuda a lokacin da kan jariri ya sauƙo zuwa ƙugun uwa. Tsawaitar naƙuda ko kuma tangarɗar naƙudar kan sa kan jariri ya danne gungun jijiyoyin laka da suka sauƙo zuwa ƙugu da ƙafafu da ake cewa “lumbosacral plexus” a yaren likita.

Duk da cewa wannan matsala tana iya shafar ƙafafu biyu a lokaci guda, amma ta fi shafar ƙafa ɗaya.

Iyaye mata da suke da haɗarin samun wannan matsala sun haɗa da:

1] Gajeru; saboda ƙuncin ƙugu.

2] Naƙuda da haihuwar jaririn da kansa ya wuce matsakaicin girma, wato girman kan jaririn ya fi faɗin mafitar ƙugun.

3] Nawa ko tsawaitar naƙuda fiye da yadda aka saba gani.

4] Uwayen da suka gaza haihuwa da kansu har sai da aka temaka musu da maƙatar ungozoma domin zaƙulo kan jaririn, wato “forcep delivery” a turance.

5] Juyewa ko karkacewar jariri yayin naƙuda da sauransu.

Alamun larurar sun haɗa da:

Waɗansu alamun suna bayyana tun a lokacin naƙuda, a yayin da wasu kuma kan bayyana bayan haihuwa.

KU KUMA KARANTA: Dalilan da ya sa maganin tazarar haihuwa ke haifar da illoli ga mata

1] Ciwo daga cinya zuwa tafin sawu.

2] Rashin jin daɗi a fatar ƙafar; kamar jin tafiyar kiyashi, jin dindiris, jin kamar ana tsira allura, ko kuma jin kamar jan wutar lantarki. 

3] Shanyewar ko raunin ƙafafu da tafin sawu.

4] Ƙwacewar fitsari da da ko bahaya.

5] Matsalar saduwa da iyali, da dai sauransu.

Sai dai, sau da yawa a kan bar iyaye matan da suka haihu a kwance saboda sun kasa tashi sakamakon rashin ƙwarin ƙafafunsu ba tare da an ɗauki matakan da suka kamata ba.
 
A yayin da mace ta haihu, sannan aka lura ta kasa taka ƙafafunta a tuntuɓi likitan fisiyo domin ɗaukar matakan da suka kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here