Khuduba: An koma cin mutuncin addini da Malamai da Shugabanni ta hanyar amfani da sabuwar fasahar AI a duniya – Sheikh Sudais

0
55
khuduba:An%20koma%20cin%20mutuncin%20addini%20da%20Malamai%20da%20Shugabanni%20ta%20hanyar%20amfani%20da%20sabuwar%20fasahar%20AI%20a%20duniya%20%E2%80%93%20Sheikh%20Sudais

KHUDUBA:An koma cin mutuncin addini da Malamai da Shugabanni ta hanyar amfani da sabuwar fasahar AI a duniya – Sheikh Sudais

Daga Shafaatu Dauda Kano

Babban limamin masallacin Harami dake birnin Makka Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais ya gargadi mutanan dake amfani da sabuwar fasahar zamani ta sadarwa wato Artificial intelligence da ake kira AI wajen yada labaran karya da juyar da tunanin jama’a ar duniya.

Sheikh Sudais yayi wannan gargadin ne a hudubarsa ta ranar Juma’a da ya gabatar a masallacin harami dake birnin Makka a Kasar Saudiyya.

Neptune prime Hausa ta rawaito cewa hudubar malamin wacce aka yada a shafin Haramain,an hango daruruwan maniyata dake da laima saboda tsananin zafin rana da aka fuskanta a birnin na Makka da kewaye.

Malamin ya buƙaci masu amfani da fasahar sadarwar ta zamani AI wajen yada labaran karya da su daina hakan ,domin gujewa fushin Ubangiji yana mai cewa kamata yayi ayi mafani da fasahar wajen samun cigaba a kowanne bangare na rayuwa.

KU KUMA KARANTA:Hukumar jindaɗin Alhazai a Kano ta fara raba kayan aikin Hajjin bana

Cikin damuwa, Sheikh Sudais yace a wannan zamani ana jirkita hotuna ko Bidiyon mahimman mutane da shugabani da malaman addini wajen yada labaran karya akansu ta hanyar amfani da fasahar ta AI.

Yace fasahar tana da amfani kuma tana da hadari.

Muna kira ga masu amfani da ita su kauce yada labaran ƙarya musamman akan aikin Hajjin bana na 2025.

Leave a Reply