Kawu Sumaila Ya canza sheƙa daga Jam’iyya NNPP Zuwa APC
Daga Shafaatu Dauda Kano
Dan majalisar dattawa daga Kano ta Kudu Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyar NNPP zuwa APC.
Kawu Sumaila ya tabbatar da haka ne a shafinsa na Facebook.
Yace eh , gaskiya ne jita jitar da ake yadawa cewa na fice daga jam’iyar NNPP zuwa APC,kuma nayi hakan ne domin na kare muradin jama’ar da nake wakilta.
KU KUMA KARANTA:Kotu ta kori ƙarar Kwankwaso da ke ƙalubalantar shugabancin NNPP
NEPTUNE PRIME Hausa ta rawaito cewa Kawu Sumaila shida wasu yan majalisar wakilai da ake zargin sun raba gari da gwamnatin kano suka gana da Shugaban jam’iyar APC na kasa Abdullahi Ganduje a Abuja.
Yan majalisar sun hada Alassan Rurum da Ali Madakin Gini da Abdullahi Sani Rogo
Saidai su yan majalisar basu sanar da komawa APC ba har Yanzu