Katsina ta zama cibiyar haɗin kan ƙabilun ƙasa a arewa — Gwamna Raɗɗa
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja.
Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina.
Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya.
KU KUMA KARANTA:Ina cikin waɗanda ƴan bindiga ke son kai wa hari — Dikko Radda
Ya ce, zaɓen wanda shi ne irin sa na farko a tarihin zaman ƙabilun Yarbawa a Arewacin ƙasar, ya nuna alamar ɗorewar haɗin kan al’ummomin ƙasa ne da ci gabansu.
Ya ce, “Wannan muhimmiyar nasara ce ga Jihar Katsina da al’ummar ƙabilun Yarbawa da ke zaune a Jihohin Arewacin ƙasa baki ɗaya.”
Da yake yi wa Aminiya ƙarin haske, Sarkin Yarbawan Jihar Kano, Oba Murtala Alimi Otisese, wanda aka zaɓa a matsayin mataimakin Sarkin Yarbawan Arewa kuma shugaba na shirye-shiryen bikin wankan sarauta, ya ce, “a ranar Lahadi mai zuwa 15 ga watan Fabrairu ne za mu gudanar da wannan biki a birnin Abuja, inda za a miƙa wa sabon Sarkin Yarbawan Arewa Oba Murtala Sani Adeleke da ’yan majalisarsa takardun shaida (Satifiket) domin tabbatar da naɗinsu a hukumance.”
Oba Murtala Alimi Otisese ya ce, “muna sa ran halartar wasu sarakunan Yarbawa da manyan mutane daga Jihohi 6 na Kudu maso Yamma da sauran shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasa zuwa wajen bikin a Abuja.”